Gwamnatin Indiya ta buƙaci WhatsApp ta dakatar da ƙaddamar da wani sabon tsari da zai bai wa masu amfani da manhajar damar amfani da sunaye na musamman (usernames) maimakon bayyana lambobin wayarsu yayin tattaunawa.

Hukumomin ƙasar sun bayyana damuwar cewa sabon tsarin na iya ƙara haɗarin zamba ta intanet da kwaikwayon mutane idan ba a samar da isassun matakan tsaro ba.

WhatsApp ta ce har yanzu ba a fara amfani da sabon tsarin ba, kuma tana aiki kan ƙarin matakan kariya, ciki har da kare sunayen manyan mutane da sanannun masu amfani da manhajar domin hana kwaikwayo da damfara.

Indiya ita ce babbar kasuwar WhatsApp a duniya, inda ake da sama da masu amfani miliyan 850, kuma gwamnatin ƙasar na ci gaba da sa ido kan yadda manyan kamfanonin fasaha ke gudanar da ayyukansu domin kare masu amfani da manhajoji.