Iran ta yi Allah-wadai da kalaman da Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya yi kan Mojtaba Khamenei, inda ta bayyana su a matsayin barazana da ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa da ya aikewa Sakatare Janar da kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A cikin wasiƙar, Iravani ya ce barazanar da aka yi wa Mojtaba Khamenei shaida ce ta abin da ya kira ta'addancin da gwamnati ke aiwatarwa, yana mai zargin cewa yin shiru da Kwamitin Tsaro ya yi na ƙara ƙarfafa Isra'ila.

Tun da farko, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce duk wata barazana da aka yi wa al'ummar Iran ko shugabanninta za ta fuskanci martani cikin gaggawa da ƙarfi.

Ya kuma bayyana cewa idan aka samu wani sabon mataki da Iran ta ɗauka a matsayin keta yarjejeniyoyin da aka cimma, ƙasarsa za ta mayar da martani kamar yadda ta dace.