Ministan Raya Matasa na Najeriya, Ayodele Olawande, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta amince da wani sabon sauyi a shirin hidimar ƙasa (NYSC), inda za a maye gurbin tufafin Khaki na yau da kullum da zanen gargajiya na Adire.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, inda ya ce matakin na da nufin ƙarfafa masana'antun cikin gida da kuma tabbatar da cewa kuɗaɗen gwamnati suna tallafa wa tattalin arzikin Najeriya.

A cewarsa, Adire ana samar da shi a cikin ƙasar, musamman a jihohin Ogun da Kwara, tare da masu sana'ar saƙa da ke da ƙwarewa wajen ƙera irin wannan zane.

"Adire na Najeriya ne. Muna da masu ƙerarsa a Ogun da Kwara. Ya kamata mu riƙa amfani da abin da ake samarwa a cikin ƙasarmu domin bunƙasa tattalin arziƙi," in ji Olawande.

Ministan ya kuma bayyana cewa, a ƙarƙashin sabon tsarin sake fasalin NYSC, za a riƙa tura masu yi wa ƙasa hidima wuraren aiki da suka dace da fannonin da suka karanta a jami'a.

Misali, waɗanda suka kammala karatun ilimi za a fi tura su makarantu domin su yi amfani da ƙwarewar da suka samu, maimakon tsarin da ake bi a baya wanda ba ya la'akari da fannin karatun masu hidimar.

Haka kuma, Olawande ya musanta rahotannin da ke cewa za a cire sojoji daga shirin NYSC. Ya ce wannan ba gaskiya ba ne, yana mai bayyana cewa sojoji za su ci gaba da taka muhimmin rawa wajen horaswa da kuma tabbatar da tsaron masu yi wa ƙasa hidima, yayin da shugabancin gudanarwar hukumar zai kasance ƙarƙashin farar hula.