Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da cewa ta tara kuɗaɗen shiga da suka kai Naira tiriliyan 3.35 tsakanin watan Janairu da Mayun shekarar 2026, yayin da take ci gaba da ƙarfafa yaƙi da fasa kwauri, sauƙaƙa harkokin kasuwanci da kuma inganta tsaron iyakokin ƙasa.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, CSC Titus Omajali, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) ya shirya a Abuja.
A cewarsa, hukumar ta sarrafa takardun shigo da kaya guda 698,817, tare da fitar da takardun tantance kaya 112,202 a cikin watanni biyar na farkon shekarar.
Ya kuma bayyana cewa an fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da darajarsu ta kai dala biliyan 1.218 ta cikin kwantena 21,376, abin da ya nuna ci gaba a fannin fitar da kaya daga Najeriya.
Game da yaƙi da fasa kwauri, Omajali ya ce jami’an Kwastam sun kama ƙwayoyin miyagun ƙwayoyi guda 375,457 a hare-hare 122, waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan 24.33 bayan biyan haraji.
Haka kuma, ya ce hukumar ta ƙwace kusan dala 789,550 da ba a bayyana ba a shari’o’i shida da suka shafi karya dokokin musayar kuɗaɗe.
Bugu da ƙari, hukumar ta kama masu safarar namun daji a shari’o’i 17, inda ta ƙwato dabbobi masu rai 104 da kuma kayayyakin namun daji iri 21.
Omajali ya jaddada cewa Hukumar Kwastam za ta ci gaba da amfani da fasahohin zamani tare da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kare iyakokin Najeriya, daƙile fasa kwauri, da kuma yaƙi da manyan laifukan ƙetare.