Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun gano tare da lalata wata haramtacciyar masana'antar ƙera makamai a Jihar Kebbi, wadda ake zargin tana da alaƙa da ayyukan ta'addanci da sauran miyagun laifuka.

A cikin wata sanarwa da jami'in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar, ya ce dakarun Rundunar Sashe ta 2 sun kai samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan da ake gudanarwa a wurin.

Ya ce a yayin samamen, sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyar da aka ƙera a gida, tare da kama mutane biyu da ake zargin suna da hannu wajen ƙerawa da safarar makamai.

A cewarsa, an gudanar da aikin ne cikin haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, kuma nasarar ta nuna ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na dakile hanyoyin samar da makamai ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma tarwatsa cibiyoyinsu a yankin Arewa maso Yamma.

Rundunar ta ƙara da cewa mutanen biyu da aka kama na ci gaba da kasancewa a tsare, inda ake yi musu tambayoyi domin gano sauran waɗanda ke da hannu a lamarin, masu ɗaukar nauyinsu, da kuma hanyoyin da ake bi wajen ƙera da safarar makaman.