Gwmanatin kano ta jaddada kudurin na Cigaba da inganta kula lafiyar yara ta hanayar raba magunguna ga kana nan yara a kananun hukumomi 36


Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan, yayin kaddamar da shirin SARMAAN 11 zagaye na uku, na rabon magunguna kyauta ga yara Yan wata daya zuwa Shekara biyar. 


Magungunan sun hadar da na gudawa da ciwon sanyi da ciwon kunne da Sauran cututtuka dake tasiri wajen nakasa yara. 


Wakilinnmu Adamu Abdullahi ya rawaito Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne cewa, Gwamnantin Kano ta tanadi akalla kwalban magani Sama da miliyan miliyan biyu da da dubu dari tara, da ma'aikata Sama da dubu Goma sha biyu biyu da zasu gabatar da aikin bada maganin a kananun hukumomi 36 dake jihar.


A karshe Kwamishina Dakta Abubakar Labaran yayi kira ga jami'an tsaro da na lafiya da al'ummar gari da cewar maganin da za a Raba kyauta ne, don haka duk inda aka gani matsawar ba a hannun jami'an dake aikin bada maganin bane a Sanar hukumomin tsaro, kuma nan take a rufe kanti ko asibitin da aka samu, sannan gwamnantin zata dauki hukunci mai tsauri akan Wanda aka samu da mallakar maganin ta gurbatacciyar hanya.