Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da fara gwajin wani sabon magani da ake fatan zai taimaka wajen yaƙi da nau'in ƙwayar cutar Ebola mai suna Bundibugyo, wadda ke ci gaba da yaɗuwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo).
Shugaban WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a ranar Alhamis cewa an yi wa majiyyaci na farko rajista domin fara gwajin maganin a ƙasar.
Alƙaluman WHO sun nuna cewa cutar ta riga ta kama sama da mutum 1,400, yayin da 438 suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar cutar.
Hukumar ta ce har yanzu babu wani allurar rigakafi ko magani da aka amince da shi don magance nau'in ƙwayar cutar Bundibugyo, wanda ke da saurin yaɗuwa kuma yana da haɗarin gaske.
WHO na gudanar da gwajin ne tare da haɗin gwiwar Cibiyar Binciken Magunguna ta Institut National de Recherche Biomédicale (INRB) da ke Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, da wata cibiyar binciken magunguna ta Belgium, da kuma Jami'ar Oxford ta Birtaniya.
An fara samun ɓarkewar wannan nau'in cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ne a watan Mayu, inda WHO ta ayyana lamarin a matsayin gaggawar lafiyar jama'a da ke buƙatar kulawa ta musamman.