Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da rabon kayayyakin kula da mata masu juna biyu da jarirai a lokacin gaggawa, da kayan haihuwa da magunguna na kimanin Naira biliyan 10 domin ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar mata da yara a Jihar Bauchi.
Wakilinnmu Adamu Abdullahi ya rawaito cewa, Ma'aikatar Lafiya da Jin Daɗin Al'umma ta Tarayya ce ta ƙaddamar da wannan shiri a ranar Asabar, da nufin rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai ta hanyar samar da kayan aikin asibiti, motocin daukar marasa lafiya (ambulance), kayan haihuwa da kuma muhimman magunguna ga cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin jihar.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al'umma mai kula da harkokin ma'aikatar, , ya ce wannan tallafi na daga cikin ƙudirin Shugaba Tinubu na inganta ayyukan kiwon lafiya a faɗin ƙasar nan.
Pate ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta zuba kimanin Naira biliyan 10 a Jihar Bauchi ta wannan shiri, yana mai cewa jihar na ci gaba da amfana da tsare-tsaren bunƙasa harkar lafiya da gwamnatin mai ci ke aiwatarwa.
Ya ce daga cikin tallafin da ake bayarwa akwai kafawa da inganta cibiyoyin lafiya na Tarayya, farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, horas da ma'aikatan lafiya masu aiki kai tsaye da marasa lafiya, da kuma samar da muhimman kayan more rayuwa na kiwon lafiya.
A cewarsa, cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 20 da ke cikin ƙananan hukumomi 15 za su karɓi kayan aikin haihuwa, waɗanda suka haɗa da na'urorin tsotse ruwa da datti (suction machines), na'urorin tara iskar oxygen (oxygen concentrators), da na'urorin auna hawan jini da kuma kayan kula da jarirai bayan haihuwa.