Wasu fitattun jaruman Kannywood na ci gaba da sanar da ficewarsu daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope, wadda aka kafa domin tallata manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Na baya-bayan nan da ya sanar da ficewarsa shi ne fitaccen jarumi Rabiu Rikadawa, wanda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya bayyana a matsayin rashin tabbas da kuma rashin bin dokoki da ƙa'idojin ƙungiyar.

A cewar Rikadawa, yadda ake tafiyar da harkokin ƙungiyar bai dace da abin da aka kafa ta a kai ba, lamarin da ya sa ya yanke shawarar ficewa.

Kafin sanarwar tasa, wasu fitattun jaruman Kannywood sun riga sun fice daga ƙungiyar, ciki har da Mansura Isa, fitaccen marubuci Ibrahim Birniwa, da kuma jarumi Yusuf Sasen.

Ficewar waɗannan fitattun mambobi ta haifar da ce-ce-ku-ce a cikin masana'antar Kannywood da kuma tsakanin masu bibiyar harkokin siyasa, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

Sai dai har yanzu shugabannin ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da ficewar mambobin nata.