Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare ƴancin gudanar da addini tare da ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabambantan addinai a faɗin ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Sakataren Hulɗa da Ƙasashe da Ƙungiyoyi na Vatican, Archbishop Paul R. Gallagher, wanda ya kai masa ziyara tare da rakiyar Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Ojukwu.
Shugaban ya ce tattaunawa da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai na daga cikin muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro da kuma ƙarfafa haɗin kan al'umma.
Ya kuma bayyana cewa yana da kyakkyawar alaƙa da Cocin Katolika tun lokacin da yake Gwamnan Jihar Legas, yana mai yabawa irin gudummawar da Cocin ke bayarwa musamman a fannonin ilimi da kiwon lafiya.
Dangane da batun tsaro, Tinubu ya ce rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a ayyukanta a baya-bayan nan, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ba ta cikakken goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.
A nasa jawabin, Archbishop Paul R. Gallagher ya bayyana cewa ya ziyarci Najeriya ne domin bikin cika shekaru 50 da kulla hulɗar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Vatican. Ya ce Najeriya na da matuƙar muhimmanci ga Cocin Katolika saboda yawan mabiya da kuma tasirin da take da shi a nahiyar Afirka.
Har ila yau, ya isar da saƙon godiya daga Paparoma Leo XIV ga Shugaba Tinubu bisa halartar bikin rantsar da shi, tare da bayyana farin cikinsa kan ci gaban da Jami'ar Veritas da Cocin Katolika ta kafa a Abuja ke samu.