Gwamnatin Iran ta ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar hutu a faɗin ƙasar domin bai wa al'umma damar halartar shirye-shiryen jana'izar jagoran addinin ƙasar, Ayatullah Ali Khamenei.

Ana sa ran gudanar da sallar jana'iza da addu'o'i a kan gawarsa da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon GMT.

A ranar Litinin kuma, za a gudanar da gagarumin taron ban-kwana, inda za a zaga da akwatin gawarsa a manyan titunan birnin Tehran. Ana sa ran miliyoyin 'yan ƙasar za su fito domin yi masa bankwana na ƙarshe.

Rahotanni sun ce za a binne Ayatullah Ali Khamenei a garinsa na haihuwa, Mashhad, a ranar Alhamis.

Kafafen yaɗa labarai na Iran sun ruwaito cewa Ayatullah Jafar Sobhani Tabrizi ne zai jagoranci sallar jana'iza da addu'o'in da za a gudanar a harabar Mosalla da ke Tehran.