Wasu 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu sun fara ɗaukar makamai domin kare kansu bayan wa'adin da ƙungiyoyin masu adawa da baƙi suka bayar na barin ƙasar ya ƙare.


Rahotanni sun ce ƙungiyoyin da ke neman korar baƙi sun kai farmaki gidaje da otal-otal da suke zargin baƙi na buya a ciki, lamarin da ya haifar da tashin hankali. An kuma tabbatar da mutuwar mutane huɗu daga ƙasashen Mozambique, Habasha da Malawi sakamakon rikicin.


Wani faifan bidiyo da ya bazu ya nuna 'yan Najeriya da wasu 'yan Afirka ta Kudu suna fuskantar juna, yayin da jami'an tsaro suka tsaya a tsakaninsu domin hana barkewar rikici. An kuma ga wasu daga cikin 'yan Najeriyar ɗauke da adduna da sauran makamai masu sauƙi, tare da jin karar harbe-harbe a wurin.


Rahotanni sun ce gwamnatocin wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Najeriya, sun shirya jigilar 'yan ƙasashensu da ke son komawa gida. Sai dai wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa ba za su bar Afirka ta Kudu ba.


Har zuwa lokacin kammala rahoton, hukumomin Najeriya da na Afirka ta Kudu ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba. Gwamnatin Najeriya ta sake kira ga hukumomin Afirka ta Kudu da su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya da ke zaune a ƙasar.