Rundunar 'Yan Sandan Jihar Sokoto ta sanar da kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne tare da ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya da harsasai masu yawa, bayan da jami'an tsaro suka dakile wani hari da aka kai ƙauyen Daraye da ke Ƙaramar Hukumar Wamako.


A cewar rundunar, an gudanar da wannan samame ne da sanyin safiyar Asabar bayan jami'an tsaro sun samu kiran gaggawa cewa dimbin 'yan bindiga masu ɗauke da manyan makamai sun mamaye ƙauyen.


A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar, DSP Ahmad Rufa'i, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an karɓi kiran gaggawar da misalin ƙarfe 1:35 na dare a ranar 4 ga Yuli, lamarin da ya sa aka gaggauta tura jami'an Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane, da Village Crime Reduction Unit (VCRU), tare da sauran ƙwararrun jami'an tsaro domin ƙarfafa jami'an da ke Hedikwatar Rundunar 'Yan Sanda ta Wamako.


Sanarwar ta bayyana cewa jami'an tsaron sun gwabza mummunan musayar wuta da maharan, lamarin da ya tilasta musu janye harin da suka kai tare da tserewa zuwa cikin daji suna ɗauke da raunukan harbin bindiga daban-daban.