Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA ta kama wata tsohuwa 'yar Najeriya mai shekaru 67 da ke zama a Birtaniya, Misis Mary Barek, bisa zargin yunƙurin safarar kilogram 13 na hodar iblis da aka ɓoye cikin bawon ayaba na bogi ta Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas.
Hukumar ta ce an kama wacce ake zargin, wadda ke aiki a matsayin mai kula da marasa lafiya a Birtaniya, a sashen masu fita na Terminal 2 na filin jirgin a ranar Lahadi, 28 ga Yuni, yayin da take ƙoƙarin hawa jirgin kamfanin Virgin Atlantic zuwa birnin Landan.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce bincike mai zurfi da aka gudanar kan jakunkunan wacce ake zargin ya kai ga gano manyan kunshi 31 na hodar iblis da aka shirya ta yadda za su yi kama da gungun ayaba, sannan aka haɗa su da sauran kayan abinci.
Babafemi ya ce, “Bincike mai zurfi da aka gudanar kan jakunkunanta ya kai ga gano manyan kunshi 31 na hodar iblis da aka shirya domin su yi kama da gungun ayaba, waɗanda nauyinsu ya kai kilogram 13. A cikin bayanin da ta bayar, tsohuwar ta amsa cewa ita ce mamallakiyar dukkan hodar iblis ɗin da aka ƙwato.”