Gwamnatin shugaba Tinubu ta musanta sakaye kudi kimanin Naira Triliyan 8 a kasafin kuɗin bara don amfani da ita a zaɓe mai zuwa.


Wannan na matsayin martani kan zargin da Atiku Abubakar Jagoran adawar ƙasar ya yi na cewa akwai wasu kuɗi da yawansu ya kai naira Triliyan 8 da wata Biliyan 8 ta daban da ba’a sanya su cikin kasafin kuɗi ba, kuma babu cikakken bayani kan abinda aka yi da su, a don haka ne yayi zargin cewa an zubasu cikin wata taskar adana kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen baɗi.


Ko da yake Atiku Abubakar yayi wannan zargi ne bisa dogaro ga rahoton asusun bayar da lamuni na IMF wanda ya fara wannan zargi, amma gwamnatin Najeriya ta ce daga IMF har Atiku basu da cikakkiyar hujja kan wannan zargi.


A cikin zargin da IMF ta yi ta bakin wakilinta a Najeriya Christian Ebeke, ya ce aƙalla kaso biyu na yawan tattalin arzikin ƙasar yayi ɓatan dabo, kuma har yanzu gwamnati bata yi bayanin yadda aka kashe waɗannan kuɗaɗe ba.


Tun bayan wannan zargi, ƴan adawa da ƙungiyoyin fararen hula suka fara chachakar gwamnati tare da matsa mata lamba kan ta yi bayanin inda kuɗaɗen suke.