Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya sanar da kafa sabuwar jam'iyyar siyasa, matakin da ya tabbatar da rabuwar siyasarsa da Firaministan ƙasar, Ousmane Sonko, wanda shi ne jagoran jam'iyyar PASTEF.
An bayyana kafa sabuwar jam'iyyar ne a wani taro da ya haɗa da ɗaruruwan magajin gari da masu goyon bayan shugaban ƙasar, yayin da ake sa ran za a yi sauye-sauye ga wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Senegal.
Sai dai babbar jam'iyyar adawa ta APR ta musanta ikirarin cewa sama da magajin gari 300 ne suka bayyana goyon bayansu ga sabuwar jam'iyyar, tana mai bayyana cewa adadin da aka fitar ba shi da tushe.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa matakin da Faye ya ɗauka na iya sauya yanayin siyasar Senegal tare da haifar da muhawara kan makomar dimokuraɗiyyar ƙasar.
Rabuwar Faye da Sonko ta biyo bayan watanni ana samun saɓani tsakanin shugabannin biyu kan yadda ake tafiyar da tattalin arzikin ƙasar da kuma batun bashin gwamnati. Rikicin ya kuma zo ne a daidai lokacin da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya dakatar da shirin bayar da rancen dala biliyan 1.8 ga Senegal.