Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da zargin cewa ta kashe sama da naira tiriliyan 8 ba tare da an tanadi kuɗin a cikin kasafin kuɗi ba, tana mai cewa an yi kuskuren fassara rahoton Asusun Lamuni na Duniya (IMF).
Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa gwamnatin ba ta da wani "kasafin kuɗi na ɓoye", yana mai jaddada cewa duk wani kuɗin da ake kashewa yana gudana ne bisa amincewar Majalisar Dokoki da kuma tanadin doka.
Ya ce wasu kashe-kashen gwamnati da suka haɗa da ayyukan raya ƙasa, biyan basussuka da kuma ayyukan gaggawa na tsaro, doka ta ba su damar gudana, don haka bai dace a bayyana su a matsayin kashe kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba.
Martanin gwamnatin ya biyo bayan rahoton IMF da ya nuna cewa wasu kashe-kashen gwamnati ba su fito fili a cikin kasafin kuɗi ba. Rahoton ya sa wasu jiga-jigan adawa, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi, suka buƙaci a gudanar da bincike kan lamarin.
Sai dai gwamnatin ta jaddada cewa IMF ba ta zarge ta da karya doka ko almundahanar kuɗi ba, illa dai ta yi tsokaci ne kan yadda ake gabatar da rahotannin kuɗaɗen gwamnati.