Ɗan Majalisar Wakilan Amurka, Riley Moore, ya ce ƙasar Amurka za ta sanya ido sosai kan yadda za a gudanar da babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.
Moore ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar NoireTV, inda aka tambaye shi ko Amurka za ta tabbatar da cewa zaɓen Najeriya mai zuwa ya kasance sahihi, adalci da kuma gaskiya.
A cewarsa, shi tare da gwamnatin Amurka za su bibiyi yadda zaɓen zai gudana, tare da lura da yadda za a aiwatar da dukkan matakan da suka shafi tsarin zaɓen.
Baya ga batun zaɓe, Moore ya bayyana cewa Majalisar Dokokin Amurka na nazarin wasu dokoki da ka iya sauya dangantakar Amurka da Najeriya.
Ya ce dokokin da ake dubawa sun shafi batutuwan da suka haɗa da kare yancin addini da kuma taimakon tsaro da Amurka ke bai wa Najeriya.