Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana dalilin da ya sa ta tsawaita wa’adin ci gaba da yin rajistar masu zaɓe (CVR) da ƙarin mako biyu a faɗin Najeriya.


Mai magana da yawun hukumar, Zainab Aminu Abubakar, ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa ƴan Najeriya da suka cancanci yin rajista amma ba su samu damar yin hakan ba ƙarin lokaci, musamman matasan da suka cika shekara 18.


A wata tattaunawa da ta yi da BBC, Aminu Abubakar ta bayyana cewa an fara aikin rijistar ne a matakai daban-daban tun daga watan Agustan shekarar 2025.


Ta ce tun farko hukumar ta tsara kammala aikin rijistar a ranar 10 ga Yuli, 2026. Sai dai bayan samun ƙorafe-ƙorafe da buƙatar ƙarin lokaci daga jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki, INEC ta yanke shawarar tsawaita wa’adin.


Sabon wa’adin da hukumar ta sanar ya nuna cewa aikin ci gaba da rijistar masu zaɓe zai ci gaba har zuwa ranar 26 ga Yuli, 2026.