Rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a wani ƙauye da ke jihar Kaduna, inda suka kashe manoma tara tare da yin garkuwa da wasu da dama.


A cewar kamfanin dillancin labarai na AFP, maharan sun kai farmakin ne a ƙauyen tare da hallaka mutane tara, sannan suka tafi da wasu mazauna yankin zuwa inda ba a sani ba.


Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da daminar bana ta fara ƙarfi, lokacin da manoma ke komawa gonakinsu domin gudanar da ayyukan noma.


Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun kai harin ne musamman kan manoman da ake zargin sun kasa biyan kuɗaɗen harajin da suka ƙaƙaba musu.


Kawo yanzu, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ko matakan da ake ɗauka domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ba.