Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu rancen da ya kai Dala biliyan 11.4 daga Bankin Duniya tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Yunin 2026, kamar yadda wani sabon bincike ya bayyana.


Binciken ya nuna cewa wannan adadi ya kai kusan kashi 78 cikin 100 na Dala biliyan 14.59 da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta samu daga Bankin Duniya cikin shekaru takwas da ta yi kan mulki.


Rahoton ya kuma bayyana cewa idan aka amince da ƙarin rancen Dala biliyan 3.19 da gwamnatin Tinubu ta nema, jimillar bashin da za ta samu daga Bankin Duniyar za ta zarce wanda aka amince wa gwamnatin Buhari.


Sai dai, duk da amincewa da rancen Dala biliyan 11.4, Bankin Duniya ya fitar da Dala biliyan 2.32 kacal zuwa yanzu. Fiye da Dala biliyan 8.4 na ci gaba da jiran cika wasu sharuɗɗa kafin a fitar da su.


Rahoton ya ce wannan ya bambanta da gwamnatin Buhari, wadda aka riga aka fitar mata da kusan kashi 82 cikin 100 na rancen da aka amince da shi.


An bayyana cewa yawancin rancen da gwamnatin Tinubu ta samu an ware su ne domin tallafa wa sauye-sauyen tattalin arziki, inganta wutar lantarki, noma, ilimi, lafiya, kare marasa ƙarfi, bunƙasa fasahar zamani da kuma samar da guraben ayyukan yi.


Masana tattalin arziki sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan yawaitar karɓo bashi. Wasu na ganin cewa rancen Bankin Duniya na da ƙarancin ruwa kuma zai iya haifar da ci gaba idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata.

Sai dai wasu sun yi gargadin cewa ci gaba da karɓo bashi na iya ƙara nauyin biyan bashin ƙasa tare da rage kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen gudanar da ayyuka.


A nata ɓangaren, Bankin Duniya ya bayyana cewa ba ya fitar da kuɗaɗen rance gaba ɗaya lokaci guda, sai dai a hankali bisa yadda ayyukan da aka ware kuɗin domin su ke gudana da kuma cika sharuɗɗan da aka amince da su tsakanin bankin da gwamnatin tarayya.