Gwamnatin tarayya ta shawarci 'yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu da ke jin rayuwarsu na cikin hadari su yi amfani da damar jiragen da gwamnati ta tanada domin komawa gida, inda jirgin ƙarshe zai isa ranar 10 ga Yuli, 2026.
Ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu Ojukwu, ta bayyana hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, tana mai cewa har yanzu babu alamun inganta tsaro sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi da ake ci gaba da kai wa a ƙasar.
Ta ce gwamnati ta nuna damuwa musamman bayan kashe wasu 'yan Najeriya biyu, Musa Yunana Joe da Charles Iroegbu, tare da buƙatar hukumomin Afirka ta Kudu su gudanar da bincike tare da hukunta masu hannu a lamarin.
Ministar ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a tsawaita aikin kwaso 'yan Najeriya bayan wa'adin ranar 30 ga Yuni domin bai wa sauran masu son dawowa damar yin hakan.
A cewarta, jirgi na huɗu ya sauke 'yan Najeriya a ranar 3 ga Yuli, yayin da wani jirgin zai tashi daga Legas zuwa Johannesburg ranar 7 ga Yuli domin ɗauko ƙarin mutane.
Ta kuma gargadi waɗanda har yanzu ba su yanke shawarar komawa gida ba da su yi la'akari da haɗarin da ke gabansu, tana mai cewa dukiya za a iya maye gurbinta, amma rayuwa ba za a iya dawo da ita ba.