Sama da mutum 10,000 ne suka nemi guraben aikin koyarwa 1,000 a makarantun firamare da Gwamnatin Jihar Nasarawa ta amince da ɗauka ƙarƙashin wani shiri na musamman da aka tanada domin inganta ilimi a yankunan karkara.


Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Nasarawa kan Harkokin Jama’a, Peter Ahemba, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na wata biyu-biyu da aka gudanar a Sakatariyar Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Nijeriya (NUJ) reshen jihar da ke Lafiya.


A cewarsa, ɗaukar malaman ya biyo bayan amincewar gwamnatin jihar da shirin samar da malamai 1,000 domin cike giɓin ƙarancin malamai da ake fama da shi a makarantun firamare, musamman a yankunan karkara.


Ya ce Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar (SUBEB) ce ta gudanar da aikin karɓar buƙatun neman aikin, inda sama da mutum 10,000 suka gabatar da takardunsu domin neman guraben.


Ahemba ya ƙara da cewa duk malaman da za a ɗauka za a tura su kai tsaye zuwa makarantun karkara domin inganta koyarwa da kuma rage matsalar ƙarancin malamai a waɗannan yankuna.