Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buƙaci masu hada-hadar man fetur a faɗin ƙasar su gaggauta rage farashin litar fetur da sauran kayayyakin mai, biyo bayan faduwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Gwamnatin ta bayyana cewa saukar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya kamata ya bayyana a farashin da ake sayar da fetur da sauran kayayyakin mai a cikin gida.
A cewar gwamnatin, babu wani dalili da zai sa a ci gaba da sayar da fetur da tsohon farashi, alhali farashin ɗanyen mai ya ragu a kasuwannin duniya.
Ta jaddada cewa rage farashin zai taimaka wajen sauƙaƙa wa ’yan Najeriya matsin tattalin arziki, tare da rage kuɗin sufuri da sauran tsadar rayuwa da ke da alaƙa da farashin man fetur.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a ɓangaren man fetur da su tabbatar sun daidaita farashin kayayyakinsu da yanayin kasuwar duniya domin amfanin masu amfani.