Matatar Man Dangote ta ci gaba da faɗaɗa kasuwancinta a duniya, bayan da ta fitar da man jirgin sama da darajarsa ta kai kusan naira biliyan 757 zuwa ƙasashen Turai a cikin watan Yuni.

Rahotanni sun nuna cewa jimillar man da aka fitar ta kai tan 466,000, wanda ya yi daidai da kusan lita miliyan 582.5, lamarin da ya zama mafi girman adadin man jirgin sama da Najeriya ta taɓa fitarwa zuwa Turai tun bayan da matatar ta fara samar da wannan nau'in mai a shekarar 2024.

Bayanan sun kuma nuna cewa Najeriya ta zama ƙasa mafi girma wajen samar wa Turai man jirgin sama a watan Yuni, inda ta fitar da tan 466,000, yayin da Amurka ta fitar da tan 399,000 kacal a daidai wannan lokaci.

Masana harkokin makamashi sun bayyana cewa wannan ci gaba na nuna yadda Matatar Dangote ke ƙara haɓaka ƙarfin tace mai da fitar da kayayyakin man fetur zuwa ƙasashen waje, tare da ƙarfafa matsayin Najeriya a kasuwannin makamashi na duniya.

Sun kuma ce nasarar na iya ƙara samar wa ƙasar kuɗaɗen shiga daga fitar da kayayyakin mai, tare da rage dogaro kan shigo da wasu kayayyakin da ake samu daga ɗanyen mai.