Gwamnatin Faransa ta tabbatar da janye dukkan jami'an diflomasiyyarta daga Burkina Faso, bayan da gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta yanke hulɗar diflomasiyya da Faransa a ƙarshen watan Yuni.
A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Faransa ta fitar, ta ce dukkan ma'aikatan ofishinta da ke Burkina Faso sun koma Faransa a ƙarshen makon da ya gabata.
Gwamnatin Burkina Faso ta yanke hulɗar ne bayan ta zargi Faransa da katsalandan cikin harkokin cikin gidanta da kuma ci gaba da tsoma baki, musamman a fannin tsaro.
Sai dai gwamnatin Faransa ta yi watsi da zarge-zargen, tana mai bayyana matakin da Burkina Faso ta ɗauka a matsayin mara tushe. Haka kuma, ta umarci jami'an diflomasiyyar Burkina Faso da su fice daga Faransa kafin ƙarshen ranar Litinin.
Tun kafin wannan mataki, Burkina Faso ta riga ta kori kimanin sojojin Faransa 400 da ke ƙasar domin taimakawa yaƙi da masu tayar da ƙayar baya. Daga bisani, gwamnatin ta karkata alaƙarta zuwa Rasha domin samun haɗin gwiwa a fannin tsaro da kayan aikin soja.
A halin da ake ciki, Faransa ta gargaɗi 'yan ƙasarta da ke zaune a Burkina Faso da su ƙara yin taka-tsantsan saboda matsalolin tsaro.
Sai dai gwamnatin Burkina Faso ta jaddada cewa saɓanin da ke tsakaninta da Faransa ya ta'allaka ne a matakin gwamnati da hulɗar diflomasiyya kawai, ba wai yana nufin katse kyakkyawar alaƙar tarihi da al'adu da ke tsakanin al'ummomin ƙasashen biyu ba.