Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta bayyana cewa hare-haren jirage marasa matuƙa a Sudan sun yi sanadin mutuwar ƙananan yara 330 a cikin watanni shida na farkon shekarar bana.
A cewar MDD, mafi yawan hare-haren sun auku ne a yankunan Darfur da Kordofan, waɗanda suka kasance cikin tsananin tasirin rikicin da ke ci gaba da addabar ƙasar.
Hukumar ta ce wannan ne adadi mafi yawa na ƙananan yara da aka kashe sakamakon hare-haren jirage marasa matuƙa tun bayan fara rikicin Sudan.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna matuƙar damuwa kan ƙarin ta'azzarar rikicin da tasirinsa ga fararen hula, musamman yara, tare da sake yin kira ga ɓangarorin da ke rikici da su mutunta dokokin yaƙi da kuma kare rayukan fararen hula.