Aƙalla sojojin Burkina Faso da kuma ƴan bangar VDP da ke taimaka musu 50 ne aka kasha, a wasu hare-hare da mayaƙan JNIM da ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda suka kai, yankuna daban daban na ƙasar a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Tuni ɗai ƙunigiyar JNIM ta ɗauki naukin kai harin, tare da wallafa wasu hotunan yadda lamarin ya faru a shafukan sada zumunta.
A cewar wata majiya, mayaƙan masu iƙirarin jihadin sun kai harin farko ne a sansanin soji da ke lardin Sourou, da misalin ƙarfe 5 na asubahin Asabar da ta gaba, inda suka kashe sojoji 23 da ƴan bangar VDP 11.
Bayaga wannan hari ƙungiyar ta kuma ɗauki nauyin kai wasu hare-hare biyu a shiyar kudu maso yamma da kuma yamma maso tsakiyar ƙasar, inda a nan kuma aka kashe aƙalla sojoji 18, yayin da aka lalata kayayyaki da dama.
Rahotanni sun nuna cewar ƴan ta’addan sun kuma saci makamai da dama a sansanonin sojin da suka farmaka, a yayin hare-haren da suka kai.
Kawo yanzu dai hukumomin Burkina Faso basu ce komai kan waɗannan hare-hare, da aka kai mabanbantan yankunan ƙasar ta yankin Sahel.