Bikin ya kunshi karrama waɗanda suka kammala shirin, tare da ƙaddamar da sabon rukuni na waɗanda za su shiga domin ci gaba da koyo hanyoyin inganta ayyukan kiwon lafiya a Najeriya.
Dayake Jawabi Gwamnan Kano Alhaji Abba kabir yusuf, Wanda kwamishinan Lafiya na Jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya wakilta, ya bayyana shirin a matsayin muhimmin yunkuri da zai taka rawa wajen samar da ƙwararrun matasa a fannin lafiya da za su taimaka wajen inganta tsarin kiwon lafiya da kuma tabbatar da ci gaban harkokin kiwon lafiya a Jihar Kano da Najeriya
Daga karshe gwamnan yayi kira ga sabbin matasan da suka samu damar Shiga rukunin na biyu na Shirin da su yi amfani da damar da suka samu wajen haɓaka iliminsu da ƙwarewar domin ba da gudummawa ga ci gaban Najeriya.