Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bayelsa ta sanar da kama wasu mutane biyu, uba da ɗansa, bisa zargin mallakar bindigogi huɗu masu harbi guda (single-barrel guns) ba bisa ƙa'ida ba.
A cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Musa Mohammed, ya fitar, ya ce jami'an sashen yaƙi da miyagun laifuka sun kama mutanen ne yayin wani aikin sintiri da binciken ababen hawa a kan titin Igbogene–Tombia da ke Yenagoa.
Sanarwar ta bayyana cewa waɗanda ake zargin sun haɗa da Tibi da ɗansa Oyabrade, dukkansu mazauna ƙaramar hukumar Ekeremor ta jihar Bayelsa.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin suna kan hanyarsu ta zuwa Abua a jihar Rivers lokacin da jami'an 'yan sanda suka tsayar da babur mai ƙafa uku (keke Napep) da suke ciki domin bincike.
A yayin binciken, jami'an sun gano bindigogi huɗu masu harbi guda da aka ɓoye a cikin buhu, inda aka rufe su da itatuwa domin kauce wa ganowa.
Rundunar ta ce an miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) da ke Yenagoa domin ci gaba da bincike, gano inda aka samo makaman da kuma tantance ko akwai wasu da ke da hannu a lamarin.
Rundunar 'yan sandan ta sake jaddada aniyarta na yaƙi da yaɗuwar makamai ba bisa ƙa'ida ba da sauran munanan laifuka a faɗin jihar.
Ta kuma yi kira ga al'umma da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.