Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da shirin noman damina na shekarar 2026, tare da fara sayar da takin zamani a farashin da gwamnati ta amince da shi, da kuma raba kayan tallafin noma kyauta ga manoma a faɗin jihar.

Tallafin ya shafi ƙananan manoma, masu rauni, matasa, mata da kuma manoman da suka koma garuruwansu bayan sun rasa matsugunansu sakamakon matsalolin tsaro.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa shirin na da nufin bunƙasa harkar noma, ƙarfafa samar da abinci, inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa zaman lafiya da ci gaban al'ummomi.

Haka kuma, gwamnatin ta jaddada aniyarta ta ci gaba da tallafa wa manoma domin ƙara yawan amfanin gona da tabbatar da wadatar abinci a jihar Borno.