Ma'aikatar Tsaro ta Tarayya ta buƙaci kamfanonin tsaro masu zaman kansu a Najeriya su rungumi amfani da fasahar zamani da tsarin tattara bayanan sirri domin ƙarfafa gudummawar da suke bayarwa wajen inganta tsaron ƙasa.

An bayyana wannan kira ne a yayin wani taron yini guda kan harkokin tsaro da aka gudanar a Abuja, inda masana tsaro, masu tsara manufofi da masu ruwa da tsaki suka tattauna hanyoyin sauya tsarin ayyukan kamfanonin tsaro daga dogaro da yawan jami'ai zuwa tsarin da ke amfani da bayanan sirri da fasahar zamani.

A cikin saƙon da ya aike wa taron, Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya shawarci masu gudanar da kamfanonin tsaro masu zaman kansu da su yi amfani da sabbin fasahohin tattara bayanai domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar.

Ya ce amfani da fasaha da bayanan sirri zai taimaka wajen gano barazana tun kafin ta faru, tare da ƙara inganta haɗin gwiwa tsakanin kamfanonin tsaro masu zaman kansu da hukumomin tsaron gwamnati.