Kotun Majistare da ke Wuse a Abuja ta yanke wa wani direba mai suna Atada Victor hukuncin yin aikin al'umma na tsawon makonni biyu, tare da biyan tarar kuɗi da diyya da suka kai Naira miliyan 1.08, bayan samunsa da laifin tukin ganganci, cin zarafin jami'in Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) da kuma sauran laifukan karya dokokin hanya.

A cikin wata sanarwa da Jami'in Yaɗa Labarai na FRSC, Osondu Ohaeri, ya sanya wa hannu, ya ce lamarin ya faru ne yayin da jami'an hukumar ke gudanar da sintiri na yau da kullum a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Sanarwar ta ce jami'an FRSC sun yi ƙoƙarin tsayar da motar direban saboda laifin karya dokar hanya, amma maimakon ya tsaya, sai ya ƙara gudun mota, inda ya buge jami'in da ke ƙoƙarin kama shi, sannan ya kutsa cikin motar sintirin FRSC domin tserewa.

Sakamakon lamarin, jami'in FRSC ya samu munanan raunuka a kai, ido da sauran sassan jikinsa.

Daga bisani an gurfanar da direban a gaban Kotun Majistare ta Wuse, inda kotun ta yanke masa hukuncin yin aikin al'umma na tsawon makonni biyu tare da biyan Naira miliyan 1.08 a matsayin tarar kuɗi da sauran haƙƙoƙin da kotu ta tanada.