Alamu na nuna cewa Najeriya da Daular Larabawa (UAE) na ƙara ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da tattalin arzikinsu, yayin da ƙasashen biyu ke kammala shirye-shiryen kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa na Dindindin domin bunƙasa haɗin gwiwarsu.
A wannan ƙoƙari ne Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Shakhboot Bin Al Nahyan, ya kai ziyarar aiki ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Talata.
Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ce ta raka baƙon ministan zuwa ganawar da shugaban ƙasar.
Da take jawabi bayan ganawar, Bianca Odumegwu-Ojukwu ta bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a faɗaɗa haɗin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen biyu, tare da amfani da damar da ke akwai domin cimma muradun ci gaba da suka yi tarayya a kansu.
Ta ƙara da cewa kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa na Dindindin zai taimaka wajen ƙarfafa alaƙa a fannoni daban-daban, ciki har da kasuwanci, zuba jari, tattalin arziki da sauran muhimman sassa na ci gaban ƙasashen biyu.