Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Harkokin Raya Yankuna ya fara bincike kan yadda Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma (NWDC) ke gudanar da harkokinta da kashe kuɗaɗenta.
'Yan majalisar sun nuna damuwa kan yadda aka kashe kusan Naira biliyan 1.19, inda suka yi zargin cewa kimanin Naira miliyan 943, wanda ya kai kusan kashi 79 cikin ɗari na adadin, an kashe su ne wajen biyan alawus-alawus na mambobin hukumar.
Kwamitin ya kuma tambayi dalilin da ya sa Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ita ce kaɗai daga cikin hukumomin raya yankuna da ba ta da daraktocin gudanarwa da kuma ma'aikata, duk da cewa an ƙaddamar da ita tun a watan Fabrairun shekarar 2025.
A martaninsu, ma'aikatar da ke sa ido kan hukumar, shugabannin hukumar da kuma Manajan Darakta sun bayyana wa kwamitin wasu ƙalubalen da ke hana hukumar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Sai dai kwamitin ya jaddada cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa domin bai wa hukumar damar cika aikinta na bunƙasa ci gaba da inganta tsaro a yankin Arewa maso Yamma.