Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta miƙa wasu kayayyakin da aka ƙwato daga hannun masu aikata laifuka ga Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, domin amfanin ɓangaren ilimi.
Kayayyakin sun haɗa da gadajen bene masu hawa biyu guda 501, katifu guda 939 da kuma gadaje na katako guda 12, waɗanda aka ƙwato yayin wani samame na musamman da EFCC ta gudanar kan masu aikata laifukan yanar gizo.
Hukumar ta bayyana cewa an danganta kayayyakin da mutane 792 da ake zargi da aikata laifuka, ciki har da baƙi 193 daga ƙasashen waje, waɗanda aka gurfanar a kotu kafin daga bisani a mayar da su ƙasashensu bayan an same su da laifi.
Da yake miƙa takardun mallakar kayayyakin ga Ministan Ilimi, Shugaban EFCC ya ce matakin ya yi daidai da manufar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta inganta tsarin ilimi da samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa ga cibiyoyin ilimi.
Ya kuma tabbatar da cewa EFCC za ta ci gaba da ƙoƙarin gano da ƙwato dukiyar da aka samu ta haramtacciyar hanya, tare da tabbatar da cewa ana amfani da ita wajen ayyukan da za su amfani al'umma.