Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) na tara sama da Naira tiriliyan 11 a matsayin kuɗaɗen shiga na shekarar 2026.
A yayin nazarin rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kwastam da Harajin Kaya, 'yan majalisar sun yaba da irin nasarorin da hukumar ta samu a shekarar kasafin kuɗi ta 2025.
Majalisar ta lura cewa Hukumar Kwastam ta zarce burin tara kuɗaɗen shiga da aka sa mata a shekarar 2025, inda ta tara Naira tiriliyan 7.2 maimakon Naira tiriliyan 6.5 da aka tsara, wanda ya nuna ƙarin sama da kashi 10 cikin ɗari.
Domin cimma sabon buri na shekarar 2026, Hukumar Kwastam ta bayyana cewa za ta ƙara amfani da fasahar zamani wajen sarrafa ayyukanta, gudanar da binciken kuɗaɗen shiga a ainihin lokaci, rage lokacin fitar da kaya da shigar da su ta kan iyakoki, tare da ƙarfafa yaƙi da safarar haramtattun kayayyaki.
Majalisar ta bayyana kwarin gwiwarta cewa waɗannan matakai za su taimaka wajen ƙara yawan kuɗaɗen shiga tare da inganta ayyukan hukumar a faɗin ƙasar.