Matatar Man Fetur ta Dangote ta fara jigilar fetur kyauta zuwa jihohi shida a faɗin Najeriya, ciki har da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Kamfanin Dangote ya sanar da fara wannan shiri ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na X a ranar Laraba.

A cewar kamfanin, shirin na da nufin sauƙaƙa isar da man fetur zuwa sassa daban-daban na ƙasar tare da inganta samar da kayayyakin man fetur ga masu amfani.

Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan tsawon lokacin da shirin zai gudana ko kuma sauran jihohin da za su ci gajiyarsa a mataki na gaba ba.

Ana sa ran wannan mataki zai taimaka wajen inganta rabon man fetur da rage wasu ƙalubalen sufuri da ake fuskanta a sassan ƙasar.