Sufeto Janar na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya sake jaddada aniyar Najeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin 'yan sanda na ƙasashe daban-daban domin bunƙasa zaman lafiya, tsaro da ci gaba mai ɗorewa a duniya.
IGP Disu ya bayyana hakan ne yayin halartar Taron Koli na Biyar na Shugabannin Hukumomin 'Yan Sanda na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNCOPS 2026), wanda aka gudanar daga ranar 7 zuwa 8 ga Yulin 2026 a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York na Amurka.
Taron ya haɗa ministoci, sufetocin janar na 'yan sanda, shugabannin hukumomin tsaro da wakilan ƙungiyoyin 'yan sanda daga sassa daban-daban na duniya domin tattauna hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya da tsaro ta hanyar haɓaka haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na ƙasa da na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Da yake jawabi a wajen taron, IGP Disu ya bayyana cewa ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka na zamani na ƙara amfani da fasahar kirkirarriyar basira (AI), hanyoyin sadarwa masu ɓoyayyen tsari da kuma fasahohin yanar gizo wajen aikata laifuka da suka zarce iyakokin ƙasashe.
Ya ce duk da irin damar da fasahar zamani ke bayarwa wajen binciken laifuka ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira, binciken bayanan dijital da fasahar gano wurare, amincewar jama'a da hukumomin tsaro ita ce ginshiƙin ingantaccen aikin 'yan sanda.
IGP Disu ya jaddada cewa amfani da fasaha dole ne ya kasance tare da tabbatar da gaskiya, riƙon amana, mutunta haƙƙin ɗan Adam da bin doka.
Haka kuma, ya yi kira ga ƙasashe mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya da su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa, horar da jami'an tsaro da kuma tabbatar da cewa duk ƙasashe suna samun damar amfani da fasahohin aikin 'yan sanda ba tare da nuna bambanci ba.
Halartar Najeriya a taron UNCOPS 2026 na nuna ci gaba da jajircewar ƙasar wajen tallafa wa ayyukan wanzar da zaman lafiya, ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na duniya da kuma yaƙi da manyan laifukan ƙetare, ta'addanci, laifukan yanar gizo da sauran barazanar tsaro da ke ƙara bayyana a duniya.