Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da tsaron Peter Obi tare da gaggauta sakin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce kare rayuka da tabbatar da 'yancin 'yan adawa nauyi ne da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ɗora wa gwamnati.

Ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta mayar da martani ga korafe-korafen Peter Obi da zage-zage ba, yana mai cewa abin da ya dace shi ne ta yi bayani cikin natsuwa tare da tabbatar da gaskiya da adalci.

Atiku ya ƙara da cewa matsalolin talauci, yunwa, rashin tsaro, cin hanci da rashawa da kuma garkuwa da mutane su ne manyan ƙalubalen da ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali a kansu, maimakon shiga takun saka da 'yan adawa.

Dangane da tsare Malam Nasir El-Rufai, Atiku ya bukaci gwamnati ta mutunta ka'idojin shari'a tare da ba shi damar samun adalci, yana mai jaddada cewa kowane ɗan Najeriya ana ɗaukarsa marar laifi ne har sai kotu ta tabbatar da akasin haka.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen ceto mutanen da aka sace tare da dawo da amincewar jama'a kan harkokin tsaro, yana mai gargadin cewa tarihi zai yi hukunci kan yadda gwamnati ta kare rayuka, haƙƙin jama'a da kuma dimokuraɗiyya.

Sai dai har zuwa lokacin fitar da wannan sanarwa, gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata martani kan kalaman Atiku Abubakar ba.