Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta ƙasa, Bello Bodejo, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin gudanar da mu'amalar kuɗaɗe da ta haura dala miliyan 2.63 ba tare da bin tanade-tanaden doka ba.

An gurfanar da Bodejo a gaban Mai Shari'a Inyang Ekwo kan tuhume-tuhume guda 12 da EFCC ta gabatar.

A cewar EFCC, ana zargin Bodejo da karɓar tsabar kuɗi dala 200,000 daga tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sa'idu Abubakar, a ranar 21 ga Janairun 2022, lamarin da hukumar ta ce ya saɓa wa dokokin da ke kayyade iyakar mu'amalar kuɗi ta tsabar kuɗi.

Hukumar ta kuma yi zargin cewa ya sake karɓar dala 100,000 daga mutumin a ranar 26 ga Oktoban 2022, tare da wasu mu'amaloli na tsabar kuɗi daban-daban da suka kai dala 980,000.

Bayan karanta tuhume-tuhumen, Bello Bodejo ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.

Lauyan EFCC, Wahab Shittu, ya buƙaci kotun ta sanya ranar fara shari'a tare da ci gaba da tsare wanda ake tuhuma.

Sai dai lauyan wanda ake ƙara, Ahmed Raji, SAN, ya sanar da kotun cewa sun riga sun shigar da buƙatar a ba shi beli, tare da roƙon kotun ta saurari buƙatar.

Kotun ta ba da umarnin ci gaba da tsare Bello Bodejo a hannun EFCC har sai an yanke hukunci kan buƙatar belinsa, sannan ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 20 ga Yuli.

A bisa doka, Bello Bodejo ana ɗaukarsa marar laifi ne har sai kotu ta tabbatar da akasin haka.