Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take ta kare kanta idan har Amurka ta ci gaba da kai mata hare-hare.
A wata tattaunawa ta waya da ya yi da Babban Hafsan Sojojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, Araqchi ya bayyana kalaman wasu jami'an Amurka na baya-bayan nan a matsayin abin da ya ce na nuna yiwuwar karya yarjejeniyoyin da aka cimma da kuma ƙara rura wutar rikici.
Ministan ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kan wasu yankuna a Iran, yana mai cewa hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma Kundin Tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya.
A cewarsa, ya gargaɗi shugaban sojojin Pakistan kan duk wani yiwuwar sabon matakin soja daga Amurka, tare da jaddada cewa Iran ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare ikon mallakar ƙasarta da tsaron al'ummarta.
Rahotanni sun ce tattaunawar ta kuma taɓo batun ƙoƙarin da Pakistan ke yi na rage zaman ɗarɗar tsakanin ɓangarorin da ke rikici.
Sai dai har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, gwamnatin Amurka ba ta fitar da wata sanarwa da ta mayar da martani kan kalaman Ministan Harkokin Wajen Iran ba.