Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama, Abuja, ta ba da umarnin tsare tsohon shugaban Kotun Ɗa'ar Ma'aikata ta Najeriya (CCT), Danladi Umar, a gidan gyaran hali na Kuje.
Mai shari'a Peter Kekemeke ne ya bayar da umarnin bayan Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi zargin cin zarafin ofis da kuma karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba.
EFCC ta yi zargin cewa Danladi Umar ya yi amfani da asusun bankin matarsa a shekarar 2021 wajen karɓar Naira miliyan 5.5 daga wani kamfani da ya samu kwangilar fentin hedikwatar Kotun Ɗa'ar Ma'aikata da ke Abuja.
Hukumar ta kuma zarge shi da sake karɓar Naira miliyan 6 ta asusun bankin matarsa a ranar 25 ga Janairun 2024 daga wani kamfani da ya gudanar da aikin inganta tsarin aikace-aikacen kotun zuwa tsarin zamani.
Bayan karanta tuhume-tuhumen, Danladi Umar ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa.
Daga nan ne Mai shari'a Peter Kekemeke ya ba da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje tare da ɗage sauraron buƙatar belinsa zuwa ranar 15 ga Yuli.
Danladi Umar ya shahara ne a lokacin da yake jagorantar shari'ar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, a lokacin da yake shugaban Kotun Ɗa'ar Ma'aikata.
A bisa doka, ana ɗaukar Danladi Umar a matsayin marar laifi har sai kotu ta tabbatar da akasin haka.