Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa mayaƙan Boko Haram na tsagin ISWAP guda shida sun miƙa wuya tare da iyalansu ga dakarun Operation Hadin Kai a jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen sun fito ne daga maɓoyar mayaƙan da ke Guduf Bubayagwa da Chikide a tsaunukan Mandara da ke ƙaramar hukumar Gwoza.
A cewarsa, dakarun sun kuma ƙwato dalar Amurka 1,120, wayoyin salula biyu kirar Tecno da wasu kayayyaki daban-daban daga hannun waɗanda suka miƙa wuya.
Hakazalika, sojojin sun kama wani mutum da ake zargi da samar wa mayaƙan ISWAP da Boko Haram kayayyaki, bayan da aka tare shi a shingen bincike na Molai a jihar Borno tare da wasu magunguna.
Kyaftin Goni ya ƙara da cewa dakarun da ke sansanin soji na Logomani a ƙaramar hukumar Ngala sun samu nasarar daƙile wani hari da ake zargin mayaƙan ISWAP sun kai a daren tsakanin ranar 6 zuwa 7 ga watan Yuli.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.