Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya gargaɗi jami'an tsaro da su guji jinkiri wajen ɗaukar mataki a kan 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane yayin gudanar da ayyukansu.

Janar Musa ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba yayin rabon motocin sulke da sauran kayan aikin tsaro ga hukumomin tsaro a jihar Sakkwato, inda ya sake jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.

Ya ce duk wani jami'in tsaro da aka tura bakin aiki bai kamata ya tsaya jiran wani ƙarin umarni ba idan ya fuskanci barazana daga 'yan ta'adda ko 'yan bindiga.

A cewarsa, duk jami'in da ya ƙi ɗaukar matakin da ya dace saboda jiran umarni za a ɗauke shi a matsayin wanda ya kasa cika nauyin da aka ɗora masa, tare da ɗaukar matakin da ya dace a kansa.

Janar Musa ya kuma bayyana cewa gwamnati ta samar da kayan aikin tsaro ne domin a yi amfani da su yadda ya kamata, yana mai kira ga jami'an tsaro da su nuna sakamako a aikace.

Sai dai ya jaddada cewa kayan yaƙi kaɗai ba za su wadatar wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro ba. Ya ce ingantattun bayanan sirri, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da kuma saurin ɗaukar mataki su ne muhimman ginshiƙai wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.