Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa mafi yawan ayyukan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kammala a Abuja tsoffin ayyuka ne da aka yi watsi da su tun gwamnatocin da suka gabata.
Da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Wike ya ce gwamnatin ta ba da fifiko wajen kammala ayyukan da ta gada kafin fara sabbin ayyuka.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin ayyukan sun shafe shekaru tsakanin 15 zuwa 16 ba a kammala su ba, amma gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba da umarnin a farfaɗo da su domin kada a bar muhimman ayyukan gwamnati su lalace.
A cewarsa, kusan kashi 60 zuwa 70 cikin 100 na ayyukan da aka kammala a cikin shekaru uku da suka gabata tsoffin ayyuka ne da aka dawo aka kammala.
Wike ya ce barin irin waɗannan ayyuka cikin halin da aka yi watsi da su yana janyo asarar dukiyar al'umma tare da hana mazauna Babban Birnin Tarayya cin gajiyar muhimman ababen more rayuwa.
Ya ƙara da cewa, baya ga kammala ayyukan da aka gada, gwamnatin FCT ta kuma ƙaddamar da sabbin ayyukan tituna da sauran ababen more rayuwa a sassa daban-daban na Abuja.
Ministan ya danganta nasarorin da ake samu a babban birnin ƙasar da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman matakin da ya ɗauka na cire Hukumar FCT daga tsarin Asusun Bai-ɗaya na Gwamnati (TSA), wanda a cewarsa ya sauƙaƙa samun kuɗaɗen gudanar da ayyukan ci gaba.