Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta wallafa jerin wasu 'yan Najeriya da take shirin kora daga ƙasar, a matsayin wani ɓangare na shirin gwamnatin Amurka na tsaurara matakan kan baƙin da ba su da takardun zama ko kuma waɗanda ake zargi ko aka samu da aikata laifuka.

A cikin sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta bayyana cewa mutanen da ke cikin jerin na hannun Hukumar Kula da Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE), inda wasu daga cikinsu ke fuskantar zarge-zargen aikata laifuka daban-daban.

Sai dai ma'aikatar ba ta bayyana ranar da za a fara aiwatar da korar mutanen ba.

A cewar DHS, matakin wani ɓangare ne na manufar gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ƙarfafa dokokin shige da fice, tare da korar baƙin da ba su da izinin zama ko waɗanda suka karya dokokin ƙasar.

Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, gwamnatin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan batun ba.

A bisa doka, duk wanda ke fuskantar zargi ana ɗaukarsa marar laifi har sai an tabbatar da laifinsa ta hanyar da doka ta tanada.