Kotun majistret mai lamba 2 ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Auwal Yusuf Sulaiman, ta fara sauraron wata ƙara da gwamnatin jihar Kano, ta gurfanar da wata mata mai suna Fatima Abdullahi wadda aka fi sani da Sele mai kimanin shekaru 20.
Ana zargin Fatima da laifin kashe saurayin ta mai suna Ismail Sidi wanda aka fi sani da Buzu.
Binciken yansanda ya bayyana cewar, a waccan rana Fatima da marigayi Ismail sun yi rigima har kuma fatiman ta bubbagawa marigayin wani abu a kansa, inda jini yayi ta zuba.
Har ila yau an kuma yi zargin cewar Fatima ta kunna wuta a gidan nata domin ta ɓatar da sawun bincike.
A zaman kotun na yau bayan karanta mata ƙunshin tuhumar ta musanta, a nan ne lauyan gwamnati Barrister Muhammad Aliyu Umar ya bayyana cewar, suna neman wata rana domin a ƙara gabatar da ita.
Lauyan ta ya roƙi kotun a kan cewar a bayar da belin ta kasancewar tana cikin hali na rashin lafiya sakamakon wuta da ta ƙone hannuwanta da ƙafafuwan ta, da kuma fuskar ta, lauyan ya bayyana cewar a daidai wannan lokaci Fatima tana buƙatar kulawar likita, inda ya dogara da sashi na 35 da na 36 na kundin tsarin mulki.
Lauyan gwamnati Muhammad Aliyu Umar ya bayyana cewar, wannan kotun ba ta da hurumin bayar da belin dangane da batun kulawar likita, a nan ma lauyan gwamnati ya bayyana cewar suna da ƙwararrun likitoci a gidan gyaran hali.
Kotun ta ɗage zaman zuwa ranar 20 ga watan Yuli, 2026, domin ta yi nazari, kotun ta kuma umarci a tsare ta zuwa waccan rana tare da bata kulawar likitoci.