Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, ya jaddada aniyar ƙasarsa ta ƙara ƙarfafa alaƙar haɗin gwiwa da Laberiya, musamman a fannonin kasuwanci, tsaro, ilimi da sufuri.

Erdoğan ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Shugaban ƙasar Laberiya, Joseph Nyuma Boakai, a birnin Istanbul.

A cewarsa, yana da muhimmanci ƙasashen biyu su ci gaba da ɗaukar matakan da za su ba su damar cin gajiyar damar da ke akwai wajen bunƙasa kasuwanci da tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa Turkiyya za ta yi aiki tare da Laberiya domin faɗaɗa haɗin gwiwa a fannoni da suka haɗa da masana'antar tsaro, harkokin tsaro, ilimi da sufuri.

Haka kuma, Shugaba Erdoğan ya taya Shugaba Joseph Boakai da al'ummar Laberiya murnar samun kujerar wucin gadi a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNSC), yana mai bayyana fatan cewa ƙasar za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa zaman lafiya da tsaro a duniya.