Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta bayyana cewa ba za ta lamunci ci gaba da buɗe masallatan Juma’a ba tare da samun amincewarta ba.


Kwamishina na Biyu a Hukumar, Sheikh Ali Danabba, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai.


Sheikh Ali Danabba ya ce doka ta tanadi cewa duk wanda ke son buɗe masallacin Juma’a dole ne ya fara neman izini daga hukumar shari’a tare da cika sharuddan da aka gindaya.


Ya jaddada cewa Hukumar ba za ta amince da duk wani yunƙuri na buɗe masallatan Juma’a ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba, yana mai kira ga al’umma da su mutunta dokoki da tsare-tsaren da aka kafa domin tabbatar da ingantaccen gudanar da harkokin ibada a jihar.


Daga bisani ya ce hukumar za ta ci gaba da sanya ido kan al’amuran da suka shafi addini domin tabbatar da komai na tafiya yadda ya kamata.